Adebayor ya samu damar barin Tottenham

Dan wasan Togo, Emmanuel Adebayor
Image caption Emmanuel ya samu izinin tafiya gida daga Tottenham, bayan mutuwar dan uwansa

Manajan kulob din Tottenham, Andres Villas-Boas ya ce, da ya bar dan wasan gaba na kulob din Emmanuel Adebayor ya koma wani kulob din a lokacin zafi.

"Ya samu dama ba sau daya ba, na ya bar kulob din, amma bai nuna sha'awa ba." Inji Villas-Boas

Dan wasan mai shekaru 29 bai buga wa Spurs wasa ba, a kakar wasannin bana.

Adebayor ya koma Spurs daga Manchester City kan kudi fam miliyan biyar a watan Agustar 2012, bayan ya yi kyakkyawan wasa a kulob din White Hart Lane, inda ya ci kwallaye 17 a gasar premier.