FIFA ta bukaci Keshi ya kare kansa

Image caption Keshi tare da sauran masu horadda Najeriya

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya-NFF ta samu wasikar koke daga FIFA game da kalaman da kocin Super Eagles, Stephen Keshi a kan kocin Malawi Tom Sainfiet.

Hukumar kwallon Malawi ce ta kai kara wajen Fifa inda tace kalaman Keshi sun nuna wariyar launin fata a kan kocin wanda asalinsa dan kasar Belgium ne.

Daga nan zuwa ranar Alhamis ake saran Keshi zai kare kansa a Fifa.

Babban jami'in NFF, Chris Green ya ce " mun samu takardar koken kuma Keshi zai kare kansa kafin cikar wa'adin".

A wasan dai Najeriya ta lallasa Malawi daci biyu da nema.

Karin bayani