Rodgers da Sturridge sun samu kyauta

Image caption Brendan Rodgers da Daniel Sturridge

Kocin Liverpool Brendan Rodgers da dan kwallonsa Daniel Sturridge sun samu kyautar Manaja da kuma dan wasan mafi bajinta a gasar Premier ta Ingila a watan Agusta.

Liverpool ce ta farko a gasar Premier kawo yanzu saboda nasarori uku da ta samu a wasanni a jere kuma Sturridge ne ya zira kwallo a duka wasannin.

Ta doke Stoke, Aston Villa da kuma Manchester United.

Wannan karo na biyu da Rodgers ya samu kyautar shi kuma Sturridge wannan ne karon farko.

A kakar wasan da ta wuce Liverpool ce ta bakwai a gasar Premier ta Ingila.

Karin bayani