2014: Najeriya za ta hadu da Habasha

Image caption Tawagar Super Eagles ta Najeriya

Ghana za ta hadu da Masar a wasan kifa daya kwala na neman gurbin zuwa gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da za a buga a Brazil a shekara ta 2014.

Zakaran kwallon Afrika, Najeriya za ta kara da kasar Habasha sai kuma Ivory Coast ta fafata da Senegal.

Tunisia kuwa zata kece raini ne da Kamaru a yayinda Burkina Faso za ta hadu da Algeria.

Za ayi bugun farko a ranar 11 zuwa 15 ga watan Okotoba sai kuma bugu na biyu a ranar 15 zuwa 19 Nuwamba.

Yadda za a fafata:

Ivory Coast v Senegal

Ethiopia v Nigeria

Tunisia v Kamaru

Ghana v Masar

Burkina Faso v Algeria

Karin bayani