Cabaye ya nemi afuwar 'yan Newcastle

Image caption Yohan Cobaye

Yohan Cabaye dake wasa a Newcastle ya nemi afuwar magoya bayan kungiyar sakamakon kin buga wasa a watan Agusta.

Cabaye mai shekaru 27, yaki amincewa ya buga wasa da West Ham a wasan da aka tashi babu ci, sakamakon kin sayar dashi ga kungiyar Arsenal lokacin da aka taya shi kan kudi kimanin fan miliyon 10.

Cabaye dan kasar Faransa, ya dawo wasa ranar Asabar data gabata, lokacin da suka kara da Aston Villa a filin wasa na St James Park.

Dan wasan ya ce, idan har magoya bayan kungiyar suna fushi dashi, to yana neman su yafe masa, kuma a shirye yake yaci gaba da bada gudun mawarsa domin kai kungiyar gaci.

Karin bayani