'A ladabtar da masu faduwa da gangan'

Image caption David Moyes

Kocin Manchester United David Moyes, ya yi kira a dauki matakin ladabtar da 'yan wasa masu faduwa a da'ira ta 18 babu dalili.

Moyes ya ce ya kamata a yi amfani da fefen bidiyo da zai taimakawa alkalan wasa na tantance dan wasan dake faduwa kasa da gangan.

Kocin ya ce ya dade yana kiraye-kiraye a kan hukunta 'yan wasa masu lambo tun yana Everton.

Shi kuwa Shugaban kungiyar Crystal Palace Steve Parish, cewa yayi a bada jan kati ga duk dan wasan da aka samu da laifin faduwa kasa da gangan.

Kiran ya biyo bayan da Ashley Young ya fadi a da'ira ta 18 da gangan alkalin wasa ya bashi kati mai dorawa a wasan da suka kara da Crystal Palace a ranar Asabar data gabata.

Karin bayani