Addo ya zama kocin Hamburg

Image caption Otto Addo

Tsohon dan kwallon kasar Ghana Otto Addo zai horadda kungiyar Hamburg na rikon kwarya sakamakon sallamar Thorsten Fink da kungiyar tayi.

Addo da yake kocin matasa 'yan kasa da shekaru 19 na Hamburg, zai gudanar da aiki tare da kocin yan wasan kar ta kwana Rodolfo Cardoso.

Addo da aka haifa a Germus ya bugawa Hamburg wasanni 14 tsakanin shekara ta 2007 da 2008.

Ya kuma bugawa Ghana wasa tsakanin 1999 zuwa 2006, ya zura kwallaye 15

Hamburg ta yanke hukuncin sallamar Think bisa rashin samun kyakkyawan sakamako da tarin matsaloli.