Kaka zai buga kwallo kyauta a AC Milan

Image caption Kaka da Robinho

Dan kwallon AC Milan Kaka ya ce ba ya son a bashi albashi a kungiyar har sai ya warke daga raunin da yake fama dashi.

Dan Brazil mai shekaru 31, an fitar da shi a wasansa na farko a kulob din a minti na 70.

A farkon wannan watanne ya koma Milan bayan ya bar kulob din zuwa Real Madrid a shekara ta 2009 a kan fan miliyan 56.

Kaka yace" Banason komai daga Milan sai dai kauna da goyon baya, har sai na murmure".

Babu tabbas ko AC Milan za ta amince da wannan bukatar.

Kaka ne gwarzon dan kwallon duniya a shekara ta 2007, kuma ya lashe gasar Serie A da AC Milan a shekara ta 2004 da kuma gasar Zakarun Turai a shekara ta 2007.

Karin bayani