Moses ya ciwa Liverpool kwallo

Image caption Victor Moses

Dan kwallon Najeriya, Victor Moses ya zira kwallo a wasansa na farko da ya bugawa Liverpool inda aka tashi biyu da biyu.

Dan wasan Swansea Jonjo Shelvey ne ya soma cin kwallo a mintuna biyu da fara wasan karfin Daniel Sturridge ya farkewa Liverpool a minti na hudu.

Victor Moses ya shigar da Liverpool a gaba kafin a tashi hutun rabin lokaci daga bisani kuma Michu ya farkewa Swansea a minti na 66.

Sai dai Liverpool ta ci gaba da rike matsayin ta farko a kan teburin gasar Premier ta Ingila da maki 10.

Karin bayani