An nada Krol a matsayin kocin Tunisia

Image caption Tutar kasar Tunisia

An nada tsohon kyaftin din Holland, Ruud Krol a matsayin kocin riko na 'yan kwallon Tunisia na tsawon watanni biyu.

Shine zai jagoranci tawagar 'yan wasan Carthage Eagles inda za su fafata da Kamaru a wasan neman cancantar buga gasar cin kofin duniya da za ayi a Brazil a shekara ta 2014.

Sai dai Krol zai ci gaba da jan ragamar kungiyar CS Sfaxien wacce ke buga gasar kwallon cikin gida na Tunisa.

Hukumar kwallon Tunisia ta nada Krol don ya maye gurbin Nabil Maaloul, wanda ya yi murabus bayan da Tunisia ta sha kashi a wajen Cape Verde daci biyu da nema.