Qatar: UEFA ta amince a sauya lokaci

Image caption Daya daga cikin filayen da za a buga gasar a Qatar

Yiwuwar buga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a shekara ta 2022 a lokacin hunturu sai kara kankama yake, bayan da shugabannin kwallon kafa a Turai suka amince kada a buga gasar lokacin bazara a kasar Qatar.

Qatar ce aka baiwa damar daukar bakuncin gasar, amma kuma zafi a lokacin bazara a kasar kan kai ma'aunin celsius 50.

Hukumar kwallon Turai-UEFA mai wakilai 54 ta dauki wannan matakinne a taron da ta keyi a Croatia.

Mataimakin Shugaban FIFA, Jim Boyce ya ce " abinda aka tattauna shine ba za a buga gasar kofin duniya a Qatar ba lokacin bazara".

Manyan jami'an FIFA ne keda alhakin daukar hukunci na karshe game da Qatar.

Ana saran a taron da zasu yi a Zurich a watan Oktoba sun amince da batun sauya lokacin gasar ta 2022.

Karin bayani