Ghana za ta kara da Masar a Kumasi

Image caption Kocin Black Stars, Kwesi Appiah

Ghana za ta kara da Masar a Kumasi a bugun farko na wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a buga a Brazil a shekara ta 2014.

Za a buga wasanne a ranar 15 ga watan Okotoba.

Hukumar kwallon ta duniya Fifa ta bada wa'adi zuwa ranar Juma'a don tabbatar da ranar wasan da kuma inda za a buga.

Za ayi bugun farko daga ranar 11 zuwa 15 ga watan Oktoba, sai kuma bugu na biyu daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Nuwamba.

Kasashen da suka samu nasara a wasannin biyu ne za su tsallake zuwa gasar kofin duniya a Brazila badi.

Karin bayani