2022: Kwamitin Olympics na jiran FIFA

Image caption Kwamatin ya ce mambobinsa sun goyi bayan sauya lokacin Gasar saboda zafin da ake yi a Qatar

Kwamitin gasar Olympics na duniya ya ce yana sa ran Fifa za ta tuntube shi game da sauya lokacin da za a buga Gasar cin kofin kwallon duniya ta shekarar 2022.

Kwamitin ya bayyana haka ne saboda a cewarsa lokacin zai iya cin karo da lokacin da za a yi gasar Olympics ta lokacin hunturu.

Za a yi wasannin Olympics na hunturu a shekarar 2022 ne a watannin Janairu da Fabrairu amma Fifa ka iya sauya lokacin gasar cin kofin kwallon duniya zuwa watannin na Janairu da Fabrairu.

Ana ganin za ta yi haka ne saboda tsoron fuskantar yanayin matsanancin zafi a kasar Qatar, wacce za ta dauki bakuncin gasar.

Kakakin kwamitin Gasar olympic ya ce,"Muna da kwarin gwiwar cewa Fifa za ta tattauna da mu a kan kwanakin da za a yi gasar domin dai mu san yadda za a bullowa lamarin ba tare da ya shafi wasannin hunturu ba''.

Karin bayani