City ta lallasa United da ci 4 - 1

Image caption Kocin City Pellegrini da kuma Moyes na United

Manchester City ta lallasa makwabciyarta Manchester United daci hudu da daya a wasan da suka buga a filin wasa na Etihad na gasar Premier ta Ingila.

Wannan ne wasan farko tsakanin makwabta tun da suka sauya masu horadda 'yan wasansu inda City ta nada Manuel Pellegrini a yayinda United ta nada David Moyes.

Sergio Aguero ne ya ciwa City kwallaye a yayinda Yaya Toure da kuma Samir Nasri suka ci kwallo daya-daya sai kuma Wayne Rooney ya farkewa United kwallo guda ana gabda tashi wasan.

Sakamakon sauran wasanni gasar Premier ta Ingila:

Arsenal 3-1 Stoke Crystal Palace 0-2 Swansea Cardiff 0-1 Tottenham Norwich 0-1 Aston Villa Liverpool 0-1 Southampton Newcastle 2-3 Hull West Brom 3-0 Sunderland West Ham 2-3 Everton Chelsea 2-0 Fulham

Karin bayani