Shearer ya yi mamakin korar Di Canio

Tsohon dan wasan Newcastle, Alan Shearer
Image caption Tsohon dan wasan Newcastle, Alan Shearer wanda a yanzu yake yi wa BBC sharhin wasanni

Korar da Sunderland ta yi wa kocinta Paolo Di Canio, bayan wasanni shida a gasar kofin Premier ta Ingila ta bana, ta baiwa Alan Shearer takaici.

Di Canio mai shekaru 45, ya samu nasarar lashe wasanni uku cikin wasanni 13, tun lokacin da aka nada shi kocin kungiyar a shekarar 2013, ya kuma samu maki daya kacal a gasar bana.

Sunderland tana matsayi na karshe a teburin, bayan da tasha kashi daci uku da nema a hannun West Brom ranar Asabar data gabata.

Shearer yace, nasha mamaki matuka domin har yanzu bai sauya halinsa ba, kuma ya kamata kungiyar ta binciki halinsa kafin ta dauke shi aiki.