Sunderland ta kori Paolo Di Canio

Image caption Paolo Di Canio

Sunderland ta kori mai horadda 'yan kwallonta Paolo Di Canio a daidai lokacin da kulob din ke na karshe a kan teburin gasar Premier ta Ingila.

Dan Italiya mai shekaru 45, ya samu nasara a wasanni uku kacal cikin 13 tunda aka nadashi koci a watan Maris, kuma kawo yanzu maki daya tal ya samu cikin wasanni biyar a gasar Premier.

Kungiyar Sunderland ta ce za ta yanke shawara kan wanda zai maye gurbin Di Canio na bada jimawa ba.

A yanzu dai Kevin Ball zai kasance kocin riko, a yayinda ake hasashen nada tsohon kocin Chelsea Di Matteo a matsayin wanda zai samu mukamin.

Korar Di Canio tasa Sunderland na kokarin nada koci na shida cikin shekaru biyar.

Karin bayani