An dage dakatarwar da aka yi wa Bility

Image caption Musa Bility

Hukumar kwallon kafa ta Afrika- CAF ta kawo karshen wa'adin watanni shida na dakatarwar da ta yiwa Shugaban hukumar kwallon kasar Liberia, Musa Bility.

An haramtawa Bility shiga harkokin kwallo ne a ranar 2 ga watan Mayu bayan da CAF ta ce ya saba ka'ida wajen amfani da wasu bayanan sirri.

A ranar Litinin, CAF ta sanar a shafinta na intanet cewar an dage dakatarwar da aka yiwa Bility ba tare da bata lokaci ba.

Bility ya kalubalanci dokokin CAF ne a kan zaben da aka baiwa Shugaban hukumar Issa Hayataou damar tsayawa takara babu hamayya.

Karin bayani