2020: Istanbul ya fi Wembley dama

Image caption Filin Wembley

Hukumar kwallon Ingila FA ta ce birnin Istanbul ne ke kan gaba wajen kokarin daukar bakuncin wasan kusada karshe da kuma na karshe a gasar cin kofin kwallon kasashen Turai da za ayi a shekara ta 2020.

Hukumar FA ta ce tanason a buga wadannan wasannin a filin Wembley, amma kuma sakatare janar na hukumar, Alex Horne ya ce Istanbul ya fi damar samun daukar bakuncin tayin la'akari da cewar birnin ya fuskancin rashin nasarar a kokarin daukar bakuncin gasar Olympics ta 2020.

Za a buga wasannin gasar Turai a 2020 a birane 13 inda kawo yanzu kasashe 32 suka nuna sha'awar daukar bakuncin gasar.

Hukumar Uefa za ta daina karbar bukatar biranen da a ranar 25 ga watan Afrilu sanna kuma ta yanke hukunci a ranar 25 ga watan Satumba.