Benteke zai yi jinyar sati shida

Christian Benteke
Image caption Raunin Benteke yazo da sauki

Dan wasan Aston Villa, Christian Benteke zai yi jinya ta sati shida saboda raunin da ya samu a kugunsa

Benteke, dan kasar Belgium ya samu raunin ne lokacin da kungiyarsa ta yi nasara da ci daya da nema a gasar Premier ranar Asabar da ta gabata.

Kazalika ba zai bugawa kasarsa wasan neman shiga kofin Duniya a watan Oktoba ba.

Kocin Aston Villa Paul Lambert ya ba da tabbacin cewa dan wasan zai yi jinya ta tsawon watanni shida, yana mai cewa sun godewa Alah tunda raunin ya zo da sauki.

An cire Villa daga kofin Capital One, bayan da ta sha kashi a hannun Tottenham har gida da ci 4 - 0.