Ibrahimovic zai kai shekarar 2016 a PSG

Dan wasan Sweden, Zlatan Ibrahimovic ya tsawaita yarjejeniyarsa da kungiyar Paris St-Germain har zuwa shekara ta 2016.

Dan shekaru 31 wanda ya hade da PSG daga AC Milan a watan Yulin shekara ta 2012, shine yafi kowanne dan wasa zira kwallo a gasar kwallon Faransa, inda yaci kwallo 30 cikin wasanni 34.

Ibrahimovic ya taimakawa PSG ta lashe gasar kwallon Faransa a karon farko tun shekerar 1994.

A hirarsa da BBC a farkon wannan watan, tsohon dan kwallon Barcelona da Juventus da kuma Ajax ya ce zai iya komawa taka leda a gasar Premier ta Ingila.

Karin bayani