London za ta karbi tseren keke a 2016

London zata karbi bakuncin tseren keke
Image caption Birnin London ya karbi gasar Olympic karo uku

An zabi birnin London domin ya karbi bakuncin gasar tseren keke ta duniya a shekara ta 2016.

A rufaffen dakin wasa na birnin na London, inda Burtnaiya ta lashe lambobin yabo guda tara a gasar Olympic a shekarar 2012, za a yi gasar tseren ta 2016.

Ministan wasanni na Burtaniy Hugh Robertson ya ce "wannan wata babbar nasara ce ga harkar wasanni a Burtaniya kuma ribar gasar Olympics ta 2012".

Rabon da birnin London ya karbi bakunicn gasar tseren kekunan tun shekara ta 1904; amma birnin Manchester ya karbi bakuncin gasar a 1996 da 2000 da 2008.

Kwamitin gudanarwa na hukumar kla da tseren kekuna ta duniya ne ya zabi birnin na London don ya karbi bakuncin gasar, a taron da kwamitin ya yi a Florence dake Italy.