Walcott zai dawo wasa a Oktoba

  • 26 Satumba 2013
Image caption Theo Walcott

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce an sami nasarar aikin da aka yi wa Theo Walcott a mararsa, har ma ana sa ran zai dawo wasa a watan gobe.

Walcott mai shekaru 24 ya yi kukan yana jin zafi a mararsa dab da karawarsu da Stoke City a Gasar Premier.

Daga bisani an yi wa dan wasan tiyata a Jamus, amma Wenger yana sa ran zai dawo wasa lokacin da Arsenal za ta kara da Norwich City ranar 19 ga watan Oktoba.

Walcott ba zai buga ba a wasan da Ingila za ta kara da Poland da Montenegro a wasan neman shiga kofin duniya.

Karin bayani