Mourinho ba abokina bane - AVB

Image caption Andre Villas-Boas da Jose Mourinho

Kocin Tottenham, Andre Villas-Boas ya ce ba ya nadamar sabawarsa da tsohon mai gidansa wato kocin Chelsea Jose Mourinho.

Villas-Boas, mai shekaru 35, ya yi aiki a karkashin Mourinho na tsawon shekaru bakwai a Porto, Chelsea da kuma Inter Milan.

A karon farko za su fuskanci juna a White Hart Lane inda Tottenham za ta dauki bakuncin Chelsea a ranar Asabar.

Villas-Boas yace " mun yi zaman lafiya a baya, amma yanzu babu abota tsakaninmu.

Sai dai Mourinho ya ki amsa tambaya a kan batun Villas-Boas lokacin da manema labarai suka tambaye shi a ranar Juma'a.

Karin bayani