Brazil: Kamaru ta gayyaci Eto'o

Image caption Samuel Etoo Fils

An gayyaci Samuel Eto'o a cikin tawagar 'yan kwallon Kamaru don buga wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da Tunisia.

Dan kwallon Chelsea din dai ya bayyana aniyarsa ta daina bugawa Kamaru kwallo inda ya sanar da yin ritaya a watan da ya gabata.

Kocin Indomitable Lions, Volker Finke ya saka sunan Eto'o a cikin tawagar 'yan kwallo 25, duk da cewar Eto'o din bai bayyana ko zai amsa gayyatar ba.

Tsohon shahararren dan kwallon Kamaru, Roger Milla ya ce zai yi kokarin shawo kan Eto'o don ya bugawa kasar kwallo.

Kamaru za ta kara da Tunisia a ranar 11 ga watan Okotoba a Tunis sai kuma ta dauki bakuncin Tunisia din a Yaounde a ranar 15 ga watan Nuwamba don neman gurbin zuwa gasar kwallon duniya a Brazil a shekara ta 2014.

Karin bayani