Messi ya bayyana a gaban kuliya

Image caption Lionel Messi

Dan kwallon Barcelona, Lionel Messi da mahaifinsa sun bayyana a gaban wata kotu a Spain bisa zargin kin biyan haraji.

Ana zargin dan wasan Argentina mai shekaru 26, wanda ya zama gwarzon dan kwallon duniya har sau hudu da shi da mahaifinsa, Jorge Messi bisa zargin kin biyan harajin fiye da Euro miliyan 4.

Ana zarginsu da amfani da kamfanonin kasashen wajen a Belize da Uruguay don sayar da wasu daga cikin tallace-tallace Messi.

Dukansu biyu sun musanta zargin wanda aka ce ya faru a shekarun 2007 zuwa 2009.

Ana saran Messi da mahaifinsa za su bayyana gaban kotun a cikin sirri a lardin Gava dake Barcelona.

Karin bayani