Nsofor na hangen komawa Ingila

Image caption Victor Obinna Nsofor

Dan kwallon Najeriya, Victor Obinna Nsofor ya kosa ya koma taka leda a gasar Premier ta Ingila, amma zai mutunta yarjejeniyarshi da kungiyar Lokomotiv Moscow.

Tsohon dan kwallon West Ham ya koma Lokomotiv ne a shekara ta 2011 bayan shafe shekara guda a Upton Park.

Dan kwallon mai shekaru 26 ya zira kwallaye takwas a wasanni 23 da ya bugawa Hammar ciki hadda kwallaye uku da ya zira wasansu da Nottingham Forest.

Obinna ya soma taka leda a nahiyar Turai a kasar Italiya tare da Chievo Verona sannan ya koma Inter Milan kafin ya je Spain da Ingila kafin ya koma Rasha.

Dan wasan Super Eagles din ba ya cikin tawagar Najeriya da ta lashe gasar kwallon kasashen Afrika a 2013.

Karin bayani