Dabi'ar Vertonghen abin kunya ne

Kocin Chelsea Jose Mourinho, ya kira dan kwallon Tottenham Jan Vertonghen da abin takaici.  Mourinho ya kira dan wasan da hakan bisa karon da sukayi da Fernando Torres.  Abin da ya yi sanadiyyar korar Torres a wasan da aka tashi 1-1, ranar Asabar a filin White Hart Lane.  Mourinho ya ce "wasu 'yan wasa suna zuwa Premier da halayyarsu wanda abin kunya ne su yi ta a kan abokan sana'arsu"  Tottenham ta sayo Vertonghen daga Ajax a shekara ta 2012, ya kuma buga mata wasanni 55.
Image caption Mourinho bai ji da din jan kati da aka baiwa Fernando Torres ba

Kocin Chelsea Jose Mourinho, ya kira dan kwallon Tottenham Jan Vertonghen da abin takaici.

Mourinho ya kira dan wasan da hakan bisa karon da sukayi da Fernando Torres.

Abin da ya yi sanadiyyar korar Torres a wasan da aka tashi 1-1, ranar Asabar a filin White Hart Lane.

Mourinho ya ce "wasu 'yan wasa suna zuwa Premier da halayyarsu wanda abin kunya ne su yi ta a kan abokan sana'arsu"

Tottenham ta sayo Vertonghen daga Ajax a shekara ta 2012, ya kuma buga mata wasanni 55.