Moyes na shakkun daukar kofin Zakaru

David Moyes Manchester United
Image caption Ferguson ya lashe kofin Premier 13 da kofin Zakaru biyu, da kofin kalubale da kofin League biyar

Kocin Manchester United David Moyes, yana tantamar ko kungiyarsa za ta iya daukar kofin Zakarun Turai.

Manchester United za ta kara da Shakhtar Donetsk ranar Laraba bayan da ta yi rashin nasara a hannun West Brom.

Wasan da ya nuna mafi munin fara gasar Premier na kungiyar a shekaru 24 da su ka wuce.

Moyes da ya karbi aikin horad da United a watan Yuli yace, "Idan za ka lashe kofin Zakaru kana bukatar gogaggun 'yan wasa biyar ko shida.''

Ya karbi aikin ne a hannun Sir Alex Ferguson, wanda ya shafe shekaru 26 yana kocin United.