Zamu casa Celtic —Alves

Daniel Alves
Image caption Wannan karon sai mun caskara Celtic

Dani Alves na Barcelona ya ce za su casa Celtic a gasar Kofin Zakaru da za su kara a satin nan.

Celtic ta Scotland ta yi galaba a kan Barcelona a bara da ci 2-1 a Parkhead, amma Alves ya ce, ''sa a suka samu, amma wannan karo mun shirya musu.''

Ya ce, ''mun yarda sun sami nasara a kanmu, amma ba fin karfinmu suka yi ba, kuma kuskuren 'yan wasanmu ne ba su fimu taka leda ba."

Ya kara da cewa sun samu nasara a wancan lokacin, amma a wannan karon hakan ba za ta faru ba.