Rodgers: Suarez da Sturridge sun fi kowa

Image caption Suarez da Sturridge

Kocin Liverpool, Brendan Rodgers ya ce 'yan wasansa na gaba Luis Suarez da Daniel Sturridge sun fi kowa a gasar Premier ta Ingila.

Sturridge ya zira kwallo sannan ya baiwa Suarez kwallaye biyu yaci inda suka doke Sunderland daci uku da daya.

Rodgers yace "babu tabbas ko akwai wadanda suka fi wadannan biyun a nan Ingila".

Kocin Liverpool yace amma hadakar 'yan wasan Manchester United Robin van Persie da Wayne Rooney abin dubawa ne.

Yanzu haka dai Liverpool ce ta biyu a kan teburin gasar Premier ta Ingila bayan an buga wasanni shida.

Karin bayani