Bale ba zai buga wasa da Copenhagen ba

Gareth Bale Injury
Image caption "Bayan gwajin da likitoci suka yi, sun sami murdewar jijiyoyi a cinyar sa ta hagu," inji Madrid

Dan kwallon Real Madrid Gareth Bale ba zai buga wasan da za su kara da FC Copenhagen a gasar kofin zakaru ta nahiyar Turai ba.

Bale, wanda aka sayo daga Tottenham a kan kudi kimanin fam miliyon 85, ya ji rauni a cinyarsa.

Dan wasan ya yi karo da wannan kaddara ce a wasan da suka yi da Athletico Madrid, wanda Athletico din ta lashe da ci 1-0 a ranar Asabar da ta gabata.

A halin da ake ciki kuma, mai tsaron raga na Madrid Iker Casillas zai yi fitowarsa ta farko a cikin watanni kusan tara a Bernabeu, bayan da ya yi jinya, Diego Lopez kuma ya maye gurbinsa.