Za a dauki hoton gwiwar Torres

Fernando Torres
Image caption Torres ya zura kwallaye 65 a wasanni 102 na gasar premier lokacin da yake kulob din Liverpool, kafin Chelsea ta saye shi a kan fam miliyan 50

A ranar Talata mai zuwa ne za a dauki hoton gwiwar dan wasan gaba na Chelsea, Ferdando Torres, bayan raunin da ya samu a karawarsu da Steaua Bucharest.

Manajan kulob din, Jose Mourinho ya ce Torres ba zai iya bin tawagar zuwa Spaniya ba, ko da yake ya na fatan raunin ba mai girma ba ne.

"Likitocin na da kwarin gwiwar cewa ba wani babban rauni bane kamar na Marco Van Ginkel, wanda zai shafe watanni shida baya buga wasa" Inji Mourinho.

Torres mai shekaru 29 dama bai yi wasan da kulob dinsa ya yi a ranar Lahadi ba, saboda dakatar da shi da aka yi a wasansu da Tottenham.