Wenger zai kara kwantiragin shekaru 3

Image caption Wenger ya sha suka daga wajen magoya bayan saboda rashin taka rawa a kasar wasa ta bana

Kocin Arsenal, Arsene Wenger, na shirin tattauna wa da Arsenal domin sabunta kwantiraginsa har tsawon shekaru uku.

Kwantiragin Wenger zai kare ne a karshen kakar bana, amma tun a baya ya sanar da niyyarsa ta ci gaba da zama a kungiyar--tuni Stan Kroenke mai rike da mafi rinjayen hannun jarin kulob din ya amince da haka.

Wenger, mai shekaru 63, ya sha fama da suka saboda rashin taka rawar gani a kakar bara, sai dai ya kai kungiyar ga nasarar samun gurbin buga Gasar cin Kofin Zakaru ta nahiyar Turai.

Tuni kungiyar ta kara karfi bayan da ta sayo Mesut Ozil, kan kudi kimanin fam miliyon 42, ya kuma taimaka mata lashe wasanni goma a jere, a duk gasar da ta buga, ciki har da Gasar cin Kofin Capital One wadda suka lashe bayan sun yi nasara a kan West Brom a bugun daga kai sai mai tsaron raga.