Ambrose ya sabunta kwangilarsa a Celtic

Image caption Efe Ambrose

Dan kwallon Celtic Efe Ambrose, ya amince da sabuwar yarjejeniyar shekaru hudu tare da zakarun kwallon Scotland.

Dan Najeriya mai shekaru 24, ya hade da Celtic ne a watan Agustan bara bayan ya bar Ashdod daga Isra'ila.

A sabuwar yarjejeniyar zai ci gaba da kasancewa tare da kulob din har zuwa shekara ta 2017.

Ambrose ya shaidawa shafin intanet ta Celtic cewar "Ina jin dadin kasancewa na tare da Celtic kuma ian farincikin tsawaita zama na tare dasu".

Karin bayani