FIFA za ta yi taro kan gasar Qatar

FIFA ta zabi Qatar ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya
Image caption An zabi Qatar daga cikin kasashe biyar da suka nemi daukar bakuncin gasar cin kofin duniya

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA za ta yi wata ganawa a ranar Juma'a, domin tattauna yiwuwar dage gasar cin kofin kwallon kafa ta shekarar 2022 da aka shirya yi a Qatar, zuwa lokacin sanyi.

An kawo shawarar sauya lokacin gasar ne saboda tsananin zafin da ake yi a kasar lokacin bazara, sai dai ana fargabar hakan zai haddasa tsaiko ga wasannin kwallon kafa na cikin gida.

Masu aiko da rahotanni sun ce da alamu za'a dauki lokaci mai tsawo ana tattaunawa, kafin amincewa a kan wata matsaya.

Haka kuma hukumar za ta yi tsokaci game da zargin da aka yi na cin zarafin 'yan cirani na kasar Nepal, dake gina guraren wasan da za a yi gasar.

Qatar ta kare kanta game da kare hakkin ma'aikata a kasar.