2022:Qatar ba ta fuskantar barazana

Image caption Daya daga cikin filayen wasan a Qatar

Hukumar kwallon kafa ta duniya-FIFA ta sanar da cewa Qatar ba ta fuskantar barazana a kan 'yancin samun daukar bakuncin gasar cin kofin duniya da za a yi shekara ta 2022.

Kasar na fuskantar wani sabon zargi kan azabtarda ma'aikata 'yan ci-rani, da kuma fargabar cewar ana yanayi mai tsananin zafi a kasar, abinda zai iya janyo matsalar ga lafiyar 'yan wasa da kuma na 'yan kallo.

Amma bisa dukkan alamu Fifa ba za ta canza matsayinta ba a kan Qatar, wacce ta samu damar bayan ta doke Australia, Japan, Koriya ta Kudu da kuma Amurka.

A yayinda za a soma taron kwanaki biyu a shalkwatar hukumar ta Fifa dake Zurich, wani wakilin a kwamitin zartar hukumar Jeffrey Webb ya shaidawa BBC cewar " muna da damar ganin an yi gyara don Qatar ta dauki bakuncin gasar a saukake".

Karin bayani