Na bar United saboda Ferguson

Paul Pogba
Image caption Paul Pogba yace ya koma Juventus domin kunyata masu cewa ba zai iya ba

Paul Pogba ya sanar da cewa ya bar Manchester United saboda kin sa shi a wasa da Alex Ferguson ya yi lokacin da suka kara da Blackburn a karshen shekara ta 2011.

Pogba mai shekarun haihuwa 20, ya yi kokarin buga wasa a babbar kungiyar, da abin ya gagara shi ne ya koma Juventus, duk da an hangi dan wasan zai zama zakara a Premier.

Dan wasan ya fadawa Ferguson lokacin da suke karawa da Blackburn "ka sani a wasan nan, zan nuna maka kwarewata" kuma a lokacin United na fama da 'yan wasa masu rauni.

Ferguson a lokacin ya ce dan wasan ba shi da da'a, tare da ejan din sa, daga baya suka tuntubi Juventus ba tare da sanin United ba.