Mourinho na murna da Chelsea

Jose Mourinho Chelsea
Image caption Chelsea ta casa Norwich har gida

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce yayi farinciki da Chelsea take cikin hudun farko a teburin premier, lokacin da aka tafi hutun makonni biyu.

Kwallayen da Eden Hazard da Willian suka zura a karshen lokaci, sun baiwa Chelsea damar lashe Norwich City 3-1 ranar Lahadi, wanda shi ne wasan farko da kungiyar ta samu nasara a waje a kofin Premier ta bana.

Chelsea ta na matsayi na uku a teburin Premier, inda mai matsayi na daya ta tsere mata da maki biyu.

Mourinho yace"An tafi hutun wasanni kuma kasancewarmu a saman tebur abu ne mai muhimmanci, kuma burinmu kenan,"