Bellamy zai daina bugawa Wales kwallo

Craig Bellamy of Wales
Image caption Bellamy zai mai da hankali wajen buga wa Cardiff kwallo

Dan wasan gaban Wales, Craige Bellamy ya sanar da cewa zai yi ritayar buga wa kasarsa wasa.

Bellamy dan kwallon Cardiff City zai yi ritaya, bayan wasan da kasarsa za ta kara da Macedoniya da Belgium, a wasannin cancantar shiga kofin duniya.

Dan wasan mai shekaru 34 a duniya, ya buga wasanni 76 ya zura kwallaye 19 a shekaru 15 da ya buga wa Wales wasa.

Bellamy zai buga wasan karshe a gida, lokacin da za su kara da Macedoni a birnin Cardiff, a wasan neman cancantar shiga kofin duniya a ranar Juma'a mai zuwa.