'Januzaj zai zabi kasarsa a nan gaba'

Januzaj Manchester United
Image caption Januzaj na thangen yana da sauran lokaci

Kocin Belgium Marc Wilmots ya ce dan kwallon Manchester United Adnan Januzaj bai yanke hukuncin ranar da zai fara buga wa kasarsa kwallo ba.

Januzaj mai shekaru 18, ya zura kwallaye biyu a wasansa na farko a United lokacin da kungiyar ta doke Sunderland da ci 2 da1 ranar Asabar.

Dan wasan zai iya buga wa kasarsa ta haihuwa, wato Belgium kwallo ko Albania ko Turkey ko kuma Serbiya.

United ta sayo Januzaj daga Anderlecht kan kudi fan 300,000.