Wenger da Ramsey sun samu kyauta

Image caption Arsene Wenger da Aaron Ramsey

An baiwa kocin Arsenal, Arsene Wenger da dan wasansa, Aaron Ramsey kyautar bajinta ta watan Satumba a gasar Premier ta Ingila.

Wenger ya samu kyautar a bangaren masu horadda 'yan wasa a yayinda aka baiwa Ramsey kyautar bangaren 'yan wasa.

Wannan ne karo na 13 da Wenger ya samu irin wannan kyautar.

Arsenal ta samu nasara a wasanninta hudu a watan Satumba a yayinda Ramsey ya zira kwallaye hudu a wasannin.

Kawo yanzu Arsenal ce ta farko a saman jadawalin gasar Premier ta Ingila.

Karin bayani