Bergkamp zai koma Arsenal

Image caption Tsohon dan kwallon Holland, Dennis Bergkamp

Tsohon dan wasan gaba na Arsenal, Denis Bergkamp ya shaidawa Telegraph sports cewa, a nan gaba zai koma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.

Bergkamp ya koma Arsenal daga InterMilana shekara ta 1995, ya buga wa kulob din wasa na tsawon shekaru 11, kuma ya dauki kofuna da dama har da kofin Premier na Ingila guda uku.

Tun lokacin da ya yi ritaya a shekarar 2006 yake marawa kungiyar baya sau da kafa, kuma ake ta rade-radin zai dawo Arsenal.

Bergkamp yanzu yana mataimakin kocin tsohuwar kungiyarsa taAjax, ya kuma ce a shirye yake ya koma Arsenal a matsayin koci, a 'yan shekaru masu zuwa.