Zamu doke Ethiopia - Amokachi

Image caption Daniel Amokachi

Mataimakin kocin Super Eagles a Nigeriya, Daniel Amokaci ya ce sun shirya tsaf domin doke Ethiopia a wasan farko na neman gurbin shiga kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci.

Amokaci ya kara da cewa Ethiopia ba kanwar lasa bace, tun da suka hawo wannan matsayin, kuma Nigeriya ce zakaran Afrika,saboda haka baza su dauki wasan zai zo da sauki ba.

Tsohon dan kwallon Najeriya kuma mataimakin koci yace sun baiwa 'yan wasan duk wani horo da ya kamata, suna kuma sa ran Najeriya zata lashe Ethiopia tun a wasan farko, ta yadda wasa na biyu zai zo da sauki.

Shima dan kwallon Super Eagles Ahmed Musa, ya ce dama ce da 'yan wasa suka samu na wakiltar kasa a kofin duniya kuma burin kowanne dan kwallo ya wakilci kasarsa.

Ethiopia za ta karbi bakuncin Nijeriya ranar Lahadi a birnin Addis Ababa a wasan farko na shiga kofin duniya.

Wasa na biyu za su kara ranar 16 ga watan Nuwamba a Calabar.