Achchakir ya nemi sassauci daga FIFA

Image caption Abderrahim Achchakir

Dan kwallon Morocco, Abderrahim Achchakir ya bukaci FIFA ta dage masa dokar hana shi kwallo na shekara daya da ta dora masa sakamakon cin zarafin alkalin wasa da ya yi.

Kotun daukaka kara ta wasanni ta tsaida ranar sauraron karar ranar 5 ga watan Nuwamba.

Achchakir ya nemi cin zarafin alkalin wasa Helder Martins de Carvalho, nan take ya bashi jan kati a wasan da aka casa su daci 3-1 a Tanzaniya a watan Maris.

FIFA ta kuma ci tararsa dalar Amurka 11,000.

Dan kwallon dake bugawa FAR Rabat mai shekaru 26, zai dawo kwallo 13 ga watan Mayu, kuma bazai buga karawa da kungiyarsa zata buga a kofin zakarun nahiyar Afrika.