Boateng ba zai bugawa Ghana ba

Image caption Kevin-Prince Boateng

Dan kwallon Ghana Kevin-Prince Boateng, ba zai buga wasan da Ghana za ta kara da Masar a wasan neman shiga kofin duniya a Kumasi, sakamakon rauni da ya samu a gwiwarsa.

Dan kwallon mai shekaru 26, ya sami rauni lokacin da yake bugawa Schalke a gasar Bundesliga ranar Asabar data gabata.

Bayan likitoci sun duba shi, sun bada shawarar a yi masa aiki a gwiwarsa ta hagu.

Kocin Ghana Kwesi Appiah bai kira dan wasan da zai maye gurbinsa ba.

Ghana ta bukaci hukumar kwallon kafa ta duniya ta sauya wajen da zasu kara da Masar sakamakon tarzoma da ake fama a babban birnin kasar.

Zagaye na biyu na wasan zasu kara ranar 19 ga watan Nuwamba a Alkahira.

Karin bayani