Rooney ya juya wa Scotland baya - Vogt

Image caption Berti Vogt

Dan kwallon Ingila Wayne Rooney, ya sami gayyatar bugawa Scotland kwallo tun yana da shekaru 16 amma yaki amincewa, in ji tsohon kocin kasar Berti Vogts.

Vogts, dan Jamus da ya jagoranci kocin Scotland daga 2002 zuwa 2004, ya ce Rooney ya cancan ci ya bugawa Scotland wasa domin kakarsa 'yar Scotland ce.

Vogts yace "na fada masa zai iya bugawa Scotland kwallo, sannan yana da shekaru 16, nan take yace min nayi hakuri domin dan Ingila ne shi.

Rooney mai shekaru 27 ya fara bugawa Ingila kwallo a Fabrairun 2003, yana da shekaru17, yanzu ya buga wasanni 84 ya zura kwallaye 84.

Karin bayani