Brazil 2014: Kasashen Afrika za su kara

Image caption Kasashe 5 ne daga Afrika zasu je Brazil

Kasashen Afrika za su buga wasannin neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya a karshen mako don hallatar gasar da za a yi a shekara ta 2014 a kasar Brazil.

A ranar Asabar Ivory Coast za ta fafata da Senegal a Abidjan a yayinda ita kuma Burkina Faso za ta kece raini tsakaninta da Algeria a birnin Ouagadougou.

Karawa tsakanin Ivory Coast da Senegal itace ta farko tsakanin kasashen biyu tun haduwarsu a Dakar a watan Okotoban 2012 inda aka dakatar da wasan saboda rikicin 'yan kallo.

A ranar Lahadi kuwa, Habasha ce za ta dauki bakuncin Najeriya a Addis Ababa sai kuma Kamaru wacce za ta kara da Tunisia.

Najeriya ta hadu da Habasha a bana lokacin gasar cin kofin Afrika inda Super Eagles ta lallasa Habash daci biyu da nema.

Karin bayani