Cece-kuce a kan nasarar Burkina Faso

Image caption Burkina Faso nada kafa daya zuwa Brazil

Ana cece-kuce game da nasarar Burkina Faso a kan Algeria daci uku da biyu a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da suka buga a Ouagadougou.

Sau biyu Algeria na farke kwalo amma a dai dai lokacin da ake wasa 2- 2, sai alkalin wasa ya baiwa Burkina Faso bugun fenariti abinda ya baiwa tawagar galaba a kan 'yan Algeria.

Da dama na ganin matakin a matsayin ya yi tsauri saboda wasu na ganin dan wasan Algeria Belkalem ya taba kwallon da kafada ne.

'Yan Algeria sun yi bore bayan wasan bisa abinda suka bayyana a matsayin rashin adalci.