Brazil: Ivory Coast ta casa Senegal

Image caption Yaya Toure da Drogba na murnar nasarar

Ivory Coast ta dauki matakin samun gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a buga a Brazil bayan ta doke Senegal daci uku da daya, a wasan da suka kara a ranar Lahadi.

Didier Drogba ne yaci kwallon farko a bugun fenariti, sai kuma Gervinho ya zira ta biyu.

Bayan an dawo hutun rabin lokacin Salomon Kalou ya ciwa Ivory Coast kwallo na uku sai kuma Papiss Demba Cisse ya farkewa Senegal ana gabda tashi wasan.

A wata mai zuwa za ayi bugu na biyu a kasar Morocco, saboda an haramtawa Senegal buga kwallo a cikin kasarta.

Karin bayani