Su wa su ka samu tikitin Brazil 2014 ?

Brazil world cup qualifiers
Image caption An fara samun kasashen da suka sami tikitin kofin duniya

Kasashen Belgium da Jermus da Colombia da Switzerland sun samu tikitin zuwa kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci 2014.

Kasashe 32, har da mai masaukin baki Brazil, za a raba zuwa rukunnai takwas da zasu kunshi kasashe hudu a kowanne rukunni da za a fidda ranar 6 Disemba a Costa do Sauipe da ke Bahia.

Sauran kasashen da suka samu tikiti sun hada da Australia da Iran da Japan da South Korea da Costa Rica da Amurka. Sai Argentina da Colombia da su ma suka samu gurbi.

A nahiyar Africa da sauran wasanni da ake sa ran kasashe biyar za su wakilce ta,